Yadda matashi ya mutu a katangar gidan da ya je yin sata a garin Bunza jihar Kebb (Bidiyo)i


Wani matashi ya gamu da ajalinsa a gidan wani mutum bayan wayar tsaro na lantarki ya kama shi a garin Bunza da ke tsakiyar jihar Kebbi.

An gan gawar matashin a katangar wani gida a Unguwar Tudun wada da ake kira Sambisa da safiyar ranar Talata 22 ga watan Fabrairu 2022, makale a kan wayar tsaro wanda yake hade da lantarki. Gawar dai ta bushe ta kangare.

Wata majiya daga Unguwar ta ce matashin ya riga ya yanke wayoyin, amma duk da haka ya gamu da ajali.

Jami'an tsaro tare da taimakon matasa a Unguwar sun sauko da gawar daga katangar gidan.

Latsa kasa ka kalli bidiyo:

https://www.facebook.com/1411221509/posts/10221699102012755/


Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN