Yadda mai mota ya take jariri mai wata 15 da haihuwa har lahira, duba dalili


Yansanda sun kama wani mai mota bayan ya take karamin yaro mai wata 15 a Duniya a hanyar DLA da ke birnin Asaba na jihar Delta. Jaridar isyaku.com ya samo.

Wani ganau ya yi zargin cewa yaron ya yi rarrafe ya fito daga shagon POS na mahaifiyarsa ne ba tare da saninta ba kafin faruwar lamarin ranar Litinin 21 ga watan Fabrairu.

Kakakin hukumar yansandan jihar Delta DSP Bright Edafe ya tabbatar da faruwar lamarin ranar Talata 22 ga watan Fabrairu.

Ya ce 'Tabbas lamarin ya faru. Shagon POS na mahaifiyar yaron mai wata 15 da haihuwa yana gaf da kofar Gate na shiga gidan mai motar. Mai motar ya iso gate ya fita daga motarsa ya bude gate domin ya shiga gida. Ba tare da sanin cewa yaron ya yi rarrafe ya shiga karkashin motar ba.

Sai mai motar ya shiga motar ya shiga gida da ita, kuma nan ya take yaron. Mun kama mai motar kuma muna gudanar da bincike" 

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN