Yadda Abubakar Malami ya yi wani abin mamaki a jihar Kebbi da ya dauki hankalin yan Najeriya


Ministan shari'a kuma Antoni janar na Najeriya Abubakar Malami SAN, yana ci gaba da haskaka rayuwar jama'ar jihar Kebbi da kyakkyawar manufofi domin inganta rayuwarsu ta hanyoyi da dama. Jaridar isyaku.com ya samo.

Wani abun mamaki shi ne yadda Abubakar Malami ya dinga aiwatar da aikin taimaka wa jama'ar jihar Kebbi sabo da Allah ba tare da neman yabo ko tukuici ba.

Ahmad Usman Mairukubta, ya samo tabbatattun ababen taimakon talakawan jihar Kebbi da Abubakar Malami ya yi kawo yanzu.

Duba ababen alhairi da Abubakar Malami ya yi wa jama'ar jihar Kebbi. 

Ya sama wa Yan jihar Kebbi aiki a :

1. Federal Commissioner, Federal Character Commission

2. Federal Commissioner, National Population Commission

3. Federal Commissioner, Federal Civil Service Commission

4. National Commissioner, Independent National Electoral Commission 

 5. Managing Director, Hydro-Electric Power Producing Areas Development Commission (HYPADEC) 

6. Chairman, National Commission for People with Disability

7. Director General, Legal Aid Council of Nigeria 

8. Executive Chairman, Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) 

9. Executive Director Finance and Administration, Sokoto Rima River Basin Development Authority (SSRBDA) 

10. Executive Director Loan, Federal Mortgage Bank of Nigeria 

11. Board Chairman, National Agency for the Prohibition of Trafficking in Persons (NAPTIP) 

12. Board Chairman, Federal Medical Center (FMC) Keffi

Abubakar Malami bai manta da Matasa ba domin kuwa ya samarwa matasa fiye da É—ari shida aiki a ma'aikatun gwamnatin Tarayya da suka haÉ—a da

1. National Drugs Law Enforcement Agency (NDLEA)

2. Nigeria Secretary and Civil Defense Corp (NSCDC) 

3. Nigerian Immigration Service (NIS) 

4. Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) 

5. Federal Fire Service

6. Central Bank of Nigeria (CBN) 

7. Federal Inland Revenue Service (FRIS) 

8. Federal Industrial Court

9. Nagerian Financial Intelligence Unit (NFIU)

10. Nigerian Export-Import Bank Bank (NEXIM)

11. Independent Currupt Practices and tier related Offices Commission (ICPC) 

12. Nigeria Correctional Services. 

Haka zalika a fannin taimakawa matasa su zamo masu dogaro dakansu Abubakar Malami bayada na biyu inda ya É—auki nauyin matasa kimanin dubu biyar (5000) koyon sanaoi hannu daban daban, goma sha biyar Æ´an asali Jihar Kebbi domin Hukuma NIGCOMSAT ta koya masu harkar VSAT

Abubakar Malami ya samar aƙalla mutanen karkara da basu gaza 3,000 ba aikin Special Public Works (SPW) na NDE

Abubakar Malami ya samarwa matasa da basu gaza 45 ba aiki Graduate Attachment Program (GAP) na NDE

Abubakar Malami ya É—auki nauyin mutum Talatin (30) domin Hukumar NITDA horar su sanin makamar aikin jarida.

Hakazalika akwai dimbin matasa Æ´an asali Jihar Kebbi dake aiki a masana'antun Abubakar Malami da suka hada da

1. Rayhan Model Academy

2. Rayhan Hotels

3. Rayhan Mall

4. Rayhan Radio.

Bisa dalilai da suka gabata ne ya sa rinjayen jama'ar jihar Kebbi ke zawarcin Abubakar Malami domin nagartaccen jagoranci da ci gaban matasa ja al'umman jihar Kebbi gaba daya. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN