Yadda mari daya kacal ya aika wata budurwa Lahira, duba abin da ya faru

Yan Mata - Ba ainihin hoton bane

Rundunar yan sanda reshen jihar Jigawa, ta kama wani magidanci ɗan shekara 40 bisa zargin kashe ɗiyarsa a ƙaramar hukumar Babura, jihar Jigawa.

Wannan na ƙunshe a wata sanarwa da kakakin yan sandan jihar, ASP Lawan Shiisu, ya fitar ranar Alhamis a Dutse, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Shiisu ya ce lamarin ya faru ranar 12 ga watan Fabrairu, 2022 a ƙauyen Achiya, bayan mutumin ya shararawa yarinyar yar shekara 11 mari.

Ya ƙara da cewa sanadin wannan marin da ya mata, yarinyar mai suna Salima Hannafi, ta rasa rayuwarta a wurin da ya mare ta.

Kakakin yan sandan ya ce:

"A ranar 12 ga watan Fabrairu, 2022 da misalin ƙarfe 10:30 na safe, wani ya kawo mana rahoton cewa, a wannan rana wani mai suna Hannafi Yakubu ɗan shekara 40 ya kashe diyarsa."

"Majiyar ta bamu bayanin cewa Hannafi ya yi amfani da hannunsa ya daki ɗiyarsa, Salima Hannafi, yar shekara 11 a ƙauyen Achiya, ƙaramar hukumar Babura."

"Sanadin haka yarinyar ta mutu nan take. Sun kai mamaciyar babban Asibitin Babura domin duba ta, a can likita ya tabbatar da rai ya yi halinsa. Mun ɗauki hotunan gawar sannan muka bayar aka mata jana'iza."

Kakakin yan sandan ya ƙara da cewa a halin yanzun hukumar yan sanda na cigaba da bincike kan lamarin kafin ɗaukar mataki.

Wata mata ta gurfanar da wani mutumi a gaban kotu kan yaƙi amincewa an ɗaura musu aure da jimawa a jihar Kaduna.

Mijin yace ya na da alaƙa da matar amma ta bariki, amma ba su kai ga auren juna ba kamar yadda ta yi ikirari

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN