Manajan gidan mai na AP2 da ke kan titin Sarki Haruna a garin Birnin kebbi ya kwashe jarkokin mai da ke ajiye a bakin fanfon mai ya jefar da su da safiyar ranar Litinin.
Biyo bayan yadda yan jarka suka cika bakin fanfo kuma hakan ya haifar da hayaniya tare da kawo cikas wajen sayar wa jama'a mai.
Bisa wannan dalili ne Manajan gidan man ya jefar da jarkokin mutane da suka ajiye jarkokinsu a bakin fanfon mai.
Hakazalika ya umarci masu sayar da mai gidan man AP2 cewa mai na N5000 ne kadai za a sayar wa masu mota, ya ce duk mai mota da bai yarda da haka ba ya fice daga gidan man.
Daga bisani dai an ci gaba da sayar da mai.
Latsa nan ka kalli bidiyon lamarin
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI