Ministan Ilimi na tarayyan Najeriya, Adamu Adamu, ya fice daga wurin tattauna wa da kungiyar daliban Najeriya (NANS) ba tare da cewa komai ba.
Channels tv ta rahoto cewan an karkare taro tsakanin bangarorin biyu ba tare da fitar da wata sanarwa game da abin da aka cimma wa ba.
Ministan ya gana da kungiyar NANS ne a wani yunkuri na kawo karshen zanga-zangar da ƴaƴan kungiyar suka fara a sassan Najeriya domin a janye yajin aiki.
Legit
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI