Yadda Kwamandojin Boko Haram 50, tare da mayaka 420 suka mika wuya ga sojoji a Borno


Jimillar mayakan ta'addanci na Boko Haram da suka mika wuya ga sojojin Najeriya sun kai 470. Daga cikin mayakan ta'addancin akwai manyan kwamandoji hamsin da iyalansu da suka mika wuya ga rundunar Operation Hadin Kai a kudancin jihar Borno, majiyoyi suka tabbatar da hakan a ranar Talata.

Wannan na zuwa ne bayan tsananin rugugi da ragargazar da sojin saman najeriya suka yi wa maboyar 'yan ta'addan da matattararsu a yankin tafkin Chadi inda suka halaka mayakan ta'addan masu tarin yawa.

Daily Trust ta tattaro cewa, 'yan ta'addan sun fito daga dajin Sambisa a ababen hawa kusan goma inda kai tsaye suka tunkari sansanin sojoji da ke Gwoza, hekwatar karamar hukumar Gwoza ta jihar.

Wata babbar majiya da rundunar sojin wacce ta san wannan cigaban ta tabbatarwa da Daily Trust cewa Birgediya kwamnandan 26 Task Force da ke Gwoza ne ya karbesu da yammacin Talata.

Aliyu Muhammad wani mazaunin Gwoza ne da ya sanar da Daily Trust ta waya cewa an ga daruruwan 'yan ta'addan a Gwoza ranar Talata.

"Sun bayyana a jigace kuam da yawa daga cikin 'ya'yansu sun bayyana a yunwace," yace.

Idan za a tuna, shugaban Boko Haram, Sheikh Abubakar Ibn Al-Shekau ya bayyana Gwoza a matsayin hedkwatar mulki ta Boko Haram a 2014, kafin dakarun sojin Najeriya su kwace garin a 2015.

Borno: Nakiyar 'yan ta'addan ISWAP ta fashe, ta halaka rayuka 6

A wani labari na daban, mutane 6 sun rasa rayukan su a ranar Litinin, baya ga mutane masu tarin yawa da suka samu raunuka, yayin da mayakan ISWAP suka dasa nakiya a hanyar Gamboru-Ngala a karamar hukumar Ngala dake jihar Borno.

Yayin zantawa da Channels Television a ranar Talata, wani ma'aikacin tallafi ya ce, al'amarin na farko ya ritsa da wata motar daukar kaya, wacce a nan take mutane uku suka rasa rayukan su.

Majiyar ta ce, fashewar nakiyar ta lashe rayukan 'yan sa kai guda biyu, wadanda suka iso wurin don kawo dauki ga wadanda suka samu rauni.

Duk da dai, sojoji da hukumomin 'yan sa kai ba su yi martani game da harin ba, har zuwa lokacin da aka tattara wannan rahoton.

Source: Legit.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN