Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta ziyarci Majalisar tarayya, duba dalili


Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta yi wa Majalisar tarayya dirar mikiya da safiyar yau domin ta shaida yadda kwamitin sake fasalin tsarin mulki zai gabatar da rahotunsa.

Majalisar dokoki na tarayya suna sake duba fasalin tsarin mulki na 1999.

Aisha Buhari ta sami rakiyar Ministan kudi da harkokin mata Zainab Ahmed da Pauline Tallen.

Wata majiya ta ce Aisha ta ziyarci Majalisar ne domin nuna goyon baya game da lamurran da suka shafi mata a Najeriya.

Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN