Yadda aka giciye saurayi a itace aka daba masa kusa a hannayensa, duba abin da ya aikata (Hotuna)


Yansanda sun ceto wani saurayi mai shekara 19 bayan an manne shi aka daba masa kusoshi a wani kututturin itace bisa zargin satar rediyo a kasar Kenya. Jaridar isyaku.com ya samo.

Wanda aka yi wa danyen hukuncin mai suna Collins Sambaya, dan asalin kauyen Chamasili ne da ke karamin gundumar Sabatia. Ya gamu da fushin wanda ya yi zargin Collins ya yi masa satar rediyo ne mai suna Elvis Irime.

Elvins tare da abokansa, ya buga wa Collins kusoshi da ake amfani da su wajen rufin kwanon gida bayan ya manne shi a wani itace da ke harabar gidan, ranar Juma'a 18 ga watan Fabrairu 2022.

Basaraken Izava na Arewa mai suna Chief Evans Endesha ne ya kira yansanda ta wayar salula. Nan take yansanda suka je wajen, sai dai Evens ya cika wandonsa da iska lokacin da ya gan yansanda.

Daga bisani yansanda sun cire kusoshi da aka buga wa Collins a hannayensa suka kai shi Asibiti inda yake samun kulawa.

A halin yanzu yansanda da masu aikin Banga sun bazu wajen neman Evans tare da abokan sa da suka daba wa Collins kusoshin a hannayensa.Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN