Mataimakin Kwamishinan yansanda Abba Kyari da ke fuskantar bincike a hannun hukumar NDLEA ya gaya wa Kotu cewa yana fama da cutar hawan jini da ciwon suga.
Kyari ya shaida wa Kotu haka ne a wani takardar neman beli da Lauyansa ta gabatar a gaban wani babban Kotun tarayya da ke Abuja.
Lauyan Kyari mai suna C.O Ikena, ta gabatar wa Kotun takardar mai lambar shari'a FHC/ANJ/CS/182/22, tana neman Kotu ta bayar da belin Abba Kyari bisa hurumin rashin lafiya.
Sai dai Alkalin Kotun mai suna Jasts Ekwo ya bukaci a gaya wa hukumar NDLEA wannan zance bayan Lauyan Kyari ya gaya wa Kotu cewa Kyari Yana hannun hukumar NDLEA a halin yanzu lokacin da Alkalin ya tambayi Lauyan Kyari cewa ina Kyari yake a halin yanzu.
Jastis Ekwo ya dage sauraron koken zuwa ranar 24 ga watan Aprilu domin ci gaba da sauraronsa.
Rubuta ra ayin ka