Yadda Abubakar Malami ya gina rijiyoyin burtsatse 236, ya sama wa mutum 5.900 N3.2b a jihar Kebbi, duba sauran


A lokacin da cutar COVID-19 ta bulla, lamari da ya haifar da kuncin tattalin arziki a tsakanin jama'a, Abubakar Malami SAN, ta kungiyarsa na jinkai KJDI, ya jagoranci nemowa, tare da samar wa jama'ar jihar Kebbi bashin ₦3.2 billion da rabawa kusan mutum 5,900 a kananan hukumomi 21 da ke fadin jihar Kebbi domin rage masu radadin kuncin tattalin arziki da lamarin ya haddasa a cikin al'umma. Shafin isyaku.com ya samo.

Kazalika, Abubakar Malami ta kungiyarsa na jinkai KJDI, ya taimaka wa jama'a da íbtila'in ambaliyar ruwa ya rutsa da su a jihar Kebbi da tallafin N16 million.

Ya kuma taimaka wa gidan rediyon Equity FM Birnin kebbi da babban injimin ban wutan lantarki 110 KVA guda daya.

Malami ta kunguyarsa na jinkai, ya gina rijiyoyin burtsatsen ruwa (Borehole) guda 236 a yankunan karkara domin amfanin jama'a a fadin jihar Kebbi.

Kadan kenan daga ayyukan jinkai da Abubakar Malami ya yi wa jama'ar jihar Kebbi. Lamari da ke zama manuniya ga alhairin tsarin lamurra, da akidarsa ta siyasa. 

Yadda Abubakar Malami ya yi wani abin mamaki a jihar Kebbi da ya dauki hankalin yan Najeriya

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN