Ta'addanci: Nan da yan kwanaki yan Najeriya zasu yi murna, Malami


Ministan Shari'a kuma Antoni Janar na ƙasar nan (AGF), Abubakar Malami, ya roki yan Najeriya su ƙara hakuri game da fallasa sunayen masu ɗaukar nauyin ta'addanci.

Yayin da yake fira da Channels tv a cikin shirin 'Siyasa a yau' ranar Litinin, Malami ya tabbatar wa yan Najeriya cewa cikin yan makonni masu zuwa mutane za su sami madogara.

Malami ya ce:

"Zaku yi farin ciki da matakan da muke É—auka a gwamnatance nan da yan makonni masu zuwa. Bayan haka, zamu tuhumi waÉ—an nan mutanen, kuma mu gurfanar da su a gaban Kotu."

Me gwamnatin Buhari take yi game da masu É—aukar nauyin ta'addanci?

Ministan ya kuma ƙara da cewa gwamnati ta maida hankali wajen shirin hukunta masu hannu a lamarin ta hanyar doka, domin aiki ne da ba zai gamu lokaci ɗaya ba.

"Wajibi mu nemi kwararan hujjoji, daga nan kuma sai mu gurfanar da su kan zargin ta'addanci."

"Ba abin da zai kasance a ɓoye, kamar yadda ake kowace shari'a a bayyane, ba abin da zai ɓuya dangane da sunayen su, alaƙar su da ta'addanci, da kuma rawar da suka taka."

Malami ya tabbatar da cewa tuni gwamnati ta kudiri aniyar ganin doka ta yi aikinta ta hukunta masu laifin da ake zargi, kamar yadda Punch ta rahoto.

FG ta gano mutum 96

Kalaman Malami kan masu É—aukar nauyin ta'addanci ya zo ne bayan gwamnatin tarayya ta ce ta gano wasu mutum 96 dake rura wutar ta'addanci da kuÉ—aÉ—en su.

Ministan labaru da al'adu, Alhaji Lai Muhammed, wanda ya faÉ—i haka ga manema labarai, yace sun gano mutanen na taimaka wa Boko Haram da yar uwarta ISWAP.

Minsitan sadarwa a Najeriya, Farfesa Isa Ali Pantami, yace yan bindiga na ribatar yawan faÉ—in kasa a jihohin arewa maso gabas wajen aikata ta'addanci.

Pantami yace hudu daga cikin jihohin Najeriya shida da suka fi faÉ—i duk suna yankin arewa maso gabas.

Legit Hausa

================

Daga Jaridar isyaku.com

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakulabari

Facebook Facebook.com/isyakulabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN