Siyasar Kebbi: Dan siyasa ya fede Dododo da raddi kan kalaman Minista


Wani Dan siyasa a jihar Kebbi Alhaji I.G. Abubakar ya ce ambaton tsagin bangaranci a jam'iyyar APC reshen jihar Kebbi tawaye ne kuma kalaman Ministan shari'a Abubakar Malami SAN dai dai suke
.

Wannan dan siyasa ya ce bai kamata mutum irin Sani Dododo ya kalubalanci kalaman Ministan sharia Abubakar Malami ba bisa ambaton tsagin su da kalaman da suka yi dai dai kuma suka dace lokacin da amfani da su ya wajaba.

Ya kara da cewa " Dododo ya yi wa Abu Geda irin wadannan kalamai a can baya, ya kuma yi wa wasu manyan Yan siyasa da suka girme shi a tarihin rayuwarsa na siyasa bisa salo irin nasa na yaudara da kalamai da yake ambato a baki amma a zuciya akasin haka ake gani"

Ya kara da cewa " Wanda bai San Dododo ba ne ya ke daukar kalamansa da muhimmanci. Domin mutum ne da rayuwarsa ta cika da tawayen siyasa akasin amana da akidar mutunci a gidan siyasa".

Ya bayar da hujja cewa " Kowa ya San cewa Sani Dododo ya yi wa Adamu Aliero tawaye a kusan karshen mulkinsa lokacin da yake Gwamnan jihar Kebbi, kuma sakamakon haka aka tasa keyarsa har Kurkuku sakamakon hujjojin doka.

Kazalika ya yi wa Saidu Nasamu Dakin gari tawaye a kusa da karshen mulkinsa lokacin mulkinsa a matsayin Gwamnan jihar Kebbi.

Ya ce "Idan har Dododo ya yi  tawaye a yanzu, babu abin mamaki a ciki saboda shikamakin halayen sa ne ya aiwatar bisa manufa".

Ya ce " Ya kamata mutane su gane cewa ta irin wadannan halaye ne Dododo ke amfanuwa da siyasa, kuma lokaci ya yi da mutane za su dawo daga rakiyar irin akidarsa na rashin alkiblar siyasa, domin dai idan ya sami abin da yake so ba zai ji kunyar sake yi wa Adamu Aliero tawaye ba kuma a gan shi kafada-kafada da tsagin Gwamnati".

================

Daga Jaridar iyaku.com

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakulabari

Facebook fFacebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN