Yan ta'adda sun sako wani dan asalin jihar Kano mai suna Muktari Ibrahim bayan iyalansa sun cika wasu sharudda masu bayar da mamaki.
Ibrahim wanda aka sace a ranar 21 ga watan Nuwamban 2021 tare da wasu matafiya a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna, ya shiga tashin hankali.
An sako shi a ranar Larabar da ta gabata bayan kwashe kusan watanni uku a wurin 'yan ta'addan kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.
An yi fansar Bakano daga hannun 'yan ta'adda da kiret 6 na giya, babura 2 da N500,000
An yi fansar Bakano daga hannun 'yan ta'adda da kiret 6 na giya, babura 2 da N500,000. Hoto daga dailynigerian.com Source: UGC
Daily Nigerian ta tattaro cewa tun bayan sace shi, iyalansa sun dinga ciniki da miyagun domin fatan a sako shi. An fara daga miliyan hamsin har suka kai dubu dari biyar, kiret shida na giya, kwali daya na maganin karfi da kuma babura 2 kirar Bajaj.
Majiyoyi daga iyalansa sun ce da farko 'yan ta'addan sun jaddada cewa a kawo musu mashin kirar Boxer guda 2 ba Bajaj ba, amma lokacin da iyalansa suka janyo hankalinsu kan haramta siyar da irin babur din a jihar, sai suka amince da hakan.
Majiyar ta ce:
"Daga bisani sun amince za su karba babur kirar Bajaj tare da kiret shida na giya, kwali daya na maganin karin karfi da kudi dubu dari biyar.
"A yayin cinikin, sun ja kunnenmu kan kada mu saka na'urar gano inda suke ko kuma mu saka guba a giyar. Ko siyan giyar, sai da muka wahala
“A yayin da aka kai musu kayayyakin bayan sa'o'i kadan da wannan tafiyar wahalan a cikin daji, sun ce za su sako dan uwan mu ne idan sun tabbatar da cewa ba a saka na'urar gane inda suke ba kuma sun gane babu guba a kayan shan.
“Daga nan sai suka sako shi washegarin da aka kai musu kayan. Ba su ba shi kudin mota ba amma sun ce ya roki wani shugaban yanki da ya kai shi hanya.
“Shugaban yankin ya jajanta masa halin da ya shiga kuma ya bashi naira dari uku, wanda yayi amfani da shi ya hau babur zuwa Zaria," daya daga cikin iyalansa wanda ya bukaci a boye sunansa ya sanar.
Legit
================
Daga Jaridar iyaku.com
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakulabari
Facebook fFacebook.com/isyakalabari
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI