Da duminsa: 'Yan ta'adda sun datse wa mutane 2 gaɓoɓi, sun sace 22, sun raunata 4 a jihar Kaduna, duba yadda ta faru


Yan ta'adda a Jihar Kaduna sun yi garkuwa da mutane 22 sun kuma raunata wasu a ranar Laraba a garin Idon da ke karamar hukumar Kajuru a jihar, Vanguard ta ruwaito.

Hakazalika, Yan sanda a Jihar Kaduna sun ce jami'ansu sun kama hatsabiban yan bindiga 2 da suka datse wa wadanda suka sace sassan jiki, kusa da kauyen Sabon-Gaya a karamar hukumar Chikun a babban hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Talata.

Amma, yan sandan ba su yi magana ba game da mutanen 22 da aka sace a Kajuru.

A cewar mutanen yankin da abin ya faru, "batagarin sun zo ne misalin karfe 12.30 na daren Laraba a lokacin da mutanen garin ke barci."
"Sun fara harbe-harbe da bindiga, suka balle kofofi da tagogi suka kwashi mutane zuwa daji."
"Ba mu san ta yadda suka zo ba kawai mun ji harbi ne suna fasa taga da kofofi. Sun zo misalin karfe 12.30 na dare."

Sunayen wadanda aka sace da wadanda aka yi wa rauni

Kansila a karamar hukumar Kajuru ya lissafa sunayen wadanda aka sace, Bala Jonathan ya bada sunan wadanda aka sace da wadanda aka yi wa rauni.

A cewarsa bayan harin, wanda aka sace sune:

"Justina Joseph, Mary Joseph, Rejoice Joseph, Stephen Joseph Samson Ladan, Christiana David, Boniface David, Helen Aminu, Mirabel Aminu, Precious Philemon, Nelson Philemon, Christian Philemon.”
"Saura sun hada da Yosi Gabriel, Stephen Clement, Jinkai Musa, Derrick Obadiah, Daniel David, Paul David, Istifanus Peter, Miracle Matthew, Jesse Charles da Favour Daniel .”
Wadanda aka yi wa raunin sune David Maigaya, Micah Musa, Josephine Matthew da Marshall Musa.”

Legit

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN