Muhimman abu 6 da ya kamata ku sani game da Jaruma Sadiya Haruna


A ranar Litinin, wata kotun Majistire dake zamanta a filin sauka da tashin jiragen sama na Mallam Aminu Kano ta yanke wa jaruma Sadiya Haruna hukuncin zaman gidan Yari tsawon wata 6 ba tare da zabin tara ba.

Daily Trust ta rahoto cewa an gurfanar da ita gaban kotun ne bisa zargin bata wa tsohon saurayinta kuma mawaƙi, Isa A. Isa, suna.

Sai dai ga dukkan alamu ba kowa yasan wasu muhimman lamurra game da jarumar ba, kuma mai jan hankali a kafar sada zumunta.

Sadiya Haruna

Muhimman abubuwa 6 da ya kamata ku sani game da Jaruma Sadiya Haruna da Kotu ta ɗaure Hoto: sayyada_sadiya_haruna Source: Instagram

Legit.ng Hausa ta tattaro muku wasu abu 6 da mai yuwu wa baku taɓa sanin su ba game da Sadiya Haruna. Gasu kamar haka:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

1. Sadiya Haruna ta fara haskakawa a shirin masana'antar Kannywood a shekarar 2017, lokacin da ta fito a fim mai suna, "Bakon Legas."

2. Sadiya ta fara jawo cece-kuce ne a shekarar 2018, okacin da ta zargi shugaban ƙungiyar jaruman Kannywood, Alhassan Kwalle, da damfararta idan ta yi yunkurin shirya wasan kwaikwayo na ƙashin kanta.

3. A wani lokaci na rayuwarta, wata kotu a jahar Kano ta umarci Sadiya Haruna ta halarci makarantar Islamiyya na tsawon watanni shida.

Kotun ta ɗauke wannan mataki kan tsohuwar jarumar ne bisa kama ta da laifin sanya abubuwan da ba su dace da da rawar batsa a shafinta na Istagram da Youtube.

4. A shekarar 2021 da ta gabata, masana'antar Shirya fina-finan Hausa wato Kannywood ta nesanta kanta da Jarumar, inda tace tun tuni Sadiya ba mamba bace a Kannywood.

5. A baya ta taɓa auren Isa A. Isa, waɓda ta jefa wa kalaman ƙarya da sharri, kuma ya ɗauki matakin maka ta gaban kotu, kuma a aka kam ta laifi, Alƙali ya tura ta zaman gida kaso na tsawon wata shida.

6. Shekaru hudu da suka gabata, Jaruma Sadiya ta fice daga Kannywood, ta maida hankali wajen kasuwanci a kafafen sada zumunta, iɓda take siyar da kayayyaki da dama.

Jarumar Kannywood, Sadiya Kabala, ta koka kan yadda mutane ke da taurin bashi idan ka amince ka ba su kayan ka.

Jarumar tace da kasuwanci ne suke samu suna tsira da mutuncin su, musamman idan suka daina harkar shirin fim.

Source: Legit.ng

================

Daga Jaridar isyaku.com

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakulabari

Facebook Facebook.com/isyakulabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN