Antoni Janar na tarayya, Abubuakar Malam, ya bayyana cewa Gwamnatin Amurka da Najeriya na tattaunawa ka yiwuwan mika dakataccen jami'an dan sanda DCP Abba Kyari bisa zargin hannun cikin almundahanan $1m.
Abubakar Malami ya bayyana cewa lallai akwai kamshin gaskiya cikin tuhumar da ake yiwa Abba Kyari.
Malami ya bayyana hakan ne yayin hira a shirin 'Politics Today' na tashar ChannelsTV ranar Litinin.
Malami yace:
"Akwai lamura da dama da ake tattaunawa kan yiwuwan mikashi da Amurka. Anan muke bukatan hadin kai."
"A iya sani na, bangarorin biyu na tattaunawa, suna hada kai kan lamarin bincike, mikashi ga Amurka, da sauran su."
"Lallai an tabbatar da kamshin gaskiya cikin zargin da ake masa kuma akwai yiwuwan gurfanar da shi da kamashi da laifi idan doka ta kamashi da laifi."
Abba Kyari da Hsuhpuppi
Yanzu-yanzu: Mun fara shawara kan mikawa gwamnatin Amurka Abba Kyari Hoto: Punch Source: Facebook
Source: Legit.ng
================
Daga Jaridar isyaku.com
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakulabari
Facebook Facebook.com/isyakulabari