Yan fashi da makami sun farmaki Bankuna da dama a garin Uromi da ke jihar Edo suka kashe mutane da dama da yammacin ranar Alhamis 24 ga watan Fabrairu, 2022. Shafin isyaku.com ya samo.
Ganau sun ce Yan fashin sun farmaki Bankuna guda 5 lokacin hari da aka gudanar cikin tsari kamar yadda majiyar ta ce.
Fayafayin bidiyo da hotunan wajen da larin ya auku sun nuna gawakin mutane cikin jini kwance a kasa.
Ana fargaban cewa an kashe akalla yansanda biyu, mace guda daya da wani mutum a wannan farmaki a adadin farko da ake yadawa a labarin harin.
Sai dai kawo yanzu babu wani bayani daga jami'an tsaro a hukumance kan lamarin.
Latsa kasa ka kalli bidiyon farmakin
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=10221117244295847&id=1086336452
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI