Da duminsa: NDLEA ta tona wa Abba Kyari asiri, ta bayyana yadda ya basu cin hancin $61,400 don su saki hodar Iblis 25kg


Hukumar hana fasa kwabrin kwayoyi a Najeriya tayi bayani filla-filla yadda ya gano dakataccen DCP na yan sandan, Abba Kyari, yana safarar kwayoyi.

Kakakin NDLEA, Femi Babafemi, a hira da manema labarai a Abuja ranar Litinin, ya ce Abba Kyari mamban kungiyar masu safarar kwayoyi daga Brazil zuwan Habasha zuwa Najeriya.

Babafemi yace Kyari ya tuntunbi wani jami'in hukumar a Junairun 2022 da a saki wasu hodar iblis da aka kama.

Ga dogon jawabin:

"Bari in yi bayani filla-filla kan abinda ya faru. Lamarin ya fara ne ranar Juma'a, 21 ga Junairu, 2022, lokacin DCP Kyari ya kira wani jami'in NDLEA dake Abuja misalin karfe 2:12 na rana. Lokacin da jami'in ya sake kira bayan mintuna biyu, Kyari yace yana son zuwa don ganinsa, don tattauna wani lamari bayan Sallar Juma'a."

"Kyari ya yarda kuma suka shirya wajen haduwa da jami'in kuma yayi bayani. Hafsoshin Jami'in sun damke wasu masu safarar kwayoyi da suka shigo Najeriya daga Habasha, da kilo 25 na hodar Iblis, a cewarsa."

"Sai ya kawo shawarar cewa a bashi kilo 15 na hodar, sannan a ajiye kilo 10 don hukunta wadanda aka kama da hodar a Enugu. Amma zai bada wani hodar Iblis na bogi domin kilo 15 don kada a gane an cire. Sai ya bukaci jami'in ya yiwa abokan aikinsa bayani."

Misalin karfe 11:05 na safiyar Litinin, 24 ga Junairu, bayan hukumar ta baiwa jami'in izinin ya cigaba da biyewa Abba Kyari, sai suka fara waya a WhatsApp tsawon rana. Shi kuma hafsan yace abokan aikinsa sun amince ayi abin."

"Sai Kyari yace zai baiwa jami'an NDLEA kudi don a sake rage kilo 5 cikin 10 na sahihin da ke hannun NDLEA, saboda ya rage kilo 5 kacal. Tunda ana sayar da kilo daya a N5m, kudin kilo 5 zai zama N35m, kuma farashin dala a ranar 24 N570/$, zai bada $61, 400."

"Sai ya (Kyari) hanzarta jami'in ya gaggauta shirya abin da Kwamdanda NDLEA na Abuja don a fito da kwayoyin da wadanda aka kama daga hannunsu a Abuja. Amma a lokacin yana Legas."

"A ranar 25 ga Junair, Abba Kyari yace zai turo kaninsa don ya kai kudin yayinda su NDLEA zasu saki wadanda aka kama, amma jami'inmu yaki yarda, yace lallai sai da Abba Kyari zai hadu. Zai jirashi ya dawo daga Legas."

"Misalin karfe 5:23 na yamma, Kyari ya koma Abuja kuma ya gana da jami'in a inda suka hadu a a baya."

"Kyari ya nuna masa yadda zasu gane hodar iblis da kwarai da za'a kaiwa NDLEA, za'ayi musu digo da jan kala. Dalilin haka shine don kada a gwada jabun hodar . Sai ya turo hotunan. A tsarinsa, idan aka gwada sahihin hodar na kilo 5 a gaban wadanda aka kama, babu bukatar gwada sauran, marasa kyan."

"Sai ya taho da kudin kilo 5 na NDELA da yayi alkawarin basu idan aka sayar, kudin $61, 400. Amma sai jami'in mu yace su shiga mota ya bashi kudin. Kuma motar na jibge da na'urar daukar bidiyo da magana."

Source: Legit.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN