Yanzu-Yanzu: An mika Abba Kyari ga NDLEA bayan kamo shi da abokan harkallarsa


Jami'in dan sandan da ake tuhuma da laifuka, DCP Abba Kyari, mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da aka dakatar ya koma hannun hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) bayan kamo shi, TheCable ta ruwaito.

A baya dai rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sanar da cafke Kyari bisa zargin alaka da wata tawagar masu safarar miyagun kwayoyi ta duniya.

An dakatar da Abba Kyari a baya domin a binciki gaskiyar zargin da FBI ta Amurka ke masa na hannu a damfarar wani balarabe a kasar Qatar tare da Hushpuppi.

Abba Kyari, dan sandan da ake zargi da harkallar kwayoyi

A ranar Litinin din da ta gabata ne dai Hukumar NDLEA ta ayyana Kyari da wasu ‘yan sanda hudu a matsayin wadanda take nema ruwa a jallo.

Femi Babafemi, mai magana da yawun hukumar ta NDLEA, ya ce hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta yi imanin cewa:

"DCP Kyari mamba ne na tawagar masu safarar miyagun kwayoyi da ke gudanar da haramtattun harkallolin kwayoyi a Brazil-Habasha-Nigeria".

Da yake magana bayan hukumar ‘yan sanda ta sanar da kama shi, Babafemi ya ce an mika Kyari da wadanda ake zargi da laifin ga NDLEA domin yi masa tambayoyi da kuma ci gaba da bincike da misalin karfe 5 na yamma.

Mutanen da aka kama tare da Abba Kyari

Biyar daga cikin wadanda ake zargi kuma aka a yanzu sun hada da:

NDLEA ta shaida cwa, wadannan jami'an duk suna hannunta bayan kame su a yau 14 ga watan Fabrairu, 2022.

Hakazalika, sanarwar ta kara da cewa:

"Hukumar na son tabbatar da cewa ba za a bar wani abu da ba za a bankado ba don tabbatar da cewa duk wadanda ake tuhuma da ke tsare da wadanda ake tuhuma a binciken cewa za su fuskanci cikakken nauyin doka a karshen binciken da ake yi."

Hukumar binciken manyan laifuka ta FBI a kasar Amurka ta tuhumi Kyari da hada baki da Hushpuppi, dan damfara na kasa da kasa, a cikin badakalar dalar Amurka miliyan 1.1, kamar yadda rahotannin da Legit.ng Hausa ta rahoto a baya.

Dan sandan da aka dakatar ya musanta zargin, yana mai cewa "hannunsa na da tsabta".

Aiki da cikawa: 'Yan sanda sun bi Abba Kyari da wasu mutane, sun kwamushe su

A wani labarin, rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama shugaban tawagar hukumar leken asiri ta IRT, DCP Abba Kyari da aka dakatar.

Jaridar Punch ta tattaro cewa, an kama shi ne tare da wasu mutane hudu ranar Litinin 14 ga watan Fabrairu.

An kama Kyari ne sa’o’i kadan bayan da hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa ta bayyana cewa tana neman sa bisa zargin alaka da safarar miyagun kwayoyi.

Source: Legit.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN