Yanzu yanzu: Wani mutum ya tsare matarsa da 'ya'yansa da bindiga, yansanda sun dira gidan...


Wani Mutumi, Felix Akeze, ma'aikacin hukumar tattara haraji ta ƙasa (FIRS) ya tsare matarsa da kuma yayansa da bindiga da nufin garkuwa a gidansa dake Chevron Drive, Lekki, jihar Legas.

Vanguard ta rahoto cewa Matar da abun ya shafa yar asalin ƙaramar hukumar Igbo Etiti, jihar Enugu, uta ta sanar da ɗan uwanta halin da suke ciki da safiyar yau.

Matar ta sanar masa da cewa.Maigidanta ya bukaci ta biya baki ɗaya kuɗin da ya kashe a kanta da kuma 'ya'yan da suka haifa ko kuma ya kashe su baki ɗaya.

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Rahotanni sun bayyana cewa jami'an tsaron dake zaune a rukunin gidanjen, wanda suka isa kofar gidan tare da yan sanda sun yi matuƙar kokari wajen samu damar shiga harabar gidan.

Jami'an tsaron da kuma yan sanda sun samu nasarar kutsa wa cikin gidan kuma suka ceto matar da kuma ƴaƴanta daga hannun mutumin.

Bayan kubutar da waɗan da abin ya shafa. matar mutumin ta bayyana cewa sun kwashe kwanaki biyar a tsare a hannun maigidanta kuma uban ƴaƴanta

Bayani na nan tafe...

Source: Legit.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN