Watanni takwas bayan Yan bindiga sun sace Yan makarantar sakandare na Kwalejin Gwamnatin tarayya su guda 80 a Birnin Yauri da ke kudancin jihar Kebbi. Har yanzu 10 daga cikinsu na hannun yan bindigan duk da kudin fansa da aka biya da kuma musanyar fursunoni da aka yi. Jaridar Daily trust ta ruwaito.
Kazalika Jaridar ta ruwaito cewa akalla Yan Mata 13 daga cikin yaran, an aurar da su ga Yan bindiga kuma wasu daga cikinsu suna da juna biyu.
Ranar 17 ga watan Yuni na 2021, Yan bindiga tsagin kasurgumin Dan bindiga Dogo Gide, sun farmaki makarantar da yaran suke a Birnin Yauri, suka dauke gomman daliban, ciki har da malamansu guda biyar.
Daily trust ta kara da cewa, akalla Yan makaranta 11 zuwa 14 ke hannun yan bindigan tsagin Gide, kuma yaro daya ne na miji a cikinsu.
Rubuta ra ayin ka