An cire kasar Rasha daga cikin gasar kwallon kofin duniya kuma an dakatad da duka kungiyoyin kwallon kasar daga duniyar kwallo sakamakon yakin da take yi da kasar Ukraniya
Hukumar kwallon duniya FIFA da hukumar kwallon Turai, UEFA suka sanar da hakan ranar Litinin.
Wannan sanarwa ya shafi dukkan kungiyoyin kwallon dake Rasha irinsu CSKA Moscow, Spartak Moscow, dss.
A cewar Jawabin hukumomin biyu: "FIFA da UEFA a yau sun yanke shawarar cewa dukkan yan kwallon Rasha, kungiyoyin kwallo da na kasa, an dakatad da su daga musharaka a wasannin FIFA da UEFA sai baba ta gani."
"Dukkan hukumomin kwallon duniya sun hada kai kan nuna goyon bayansu ga al'ummar kasar Ukraine."
Shugabannin hukumomin biyu (Gianni Infantino da Aleksander Ceferin) na kyautata zaton cewa lamarin yaki zai yi sauki kuma a dawo zaman lafiya da ake."
Source: Legit.ng
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI