Daya daga cikin fitattun malaman addinin Musulunci a Masar, shehin Al Azhar, ya ce ya kamata a sake duba fatawar da ta kara wa matan aure yawan kaso na gado bayan mazansu sun mutu.
Sheikh Ahmed el-Tayeb ya ce ya zama wajibi a koma kan fatawar, a wannan zamani da ya tilasta wa mata yin aiki domin tallafa wa iyalansu.
Fatawar za ta ba matan aure damar karbar wani kaso mai tsoka na dukiyar gado bayan mutuwar mijinsu.
A karkashin shari'ar Musulunci, ana ba mace kashi daya cikin hudu na dukiyar gadon mijinta idan mamacin ba shi da 'ya'ya, amma akan ba ta kashi daya cikin takwas idan yana da 'ya'ya.
BBC