Sanata Dino Melaye wanda ya wakilci Kogi ta yamma a majalisar dattawa ya yi ikirarin magoya bayan Kamaru sun jibgi 'yan wasansu a gasar AFCON.
The Cable ta ce hakan na zuwa ne bayan ‘yan kwallon Masar sun doke na kasar Kamaru a gasar cin kofin Afrika a filin wasan Olembe da ke Yaounde.
Bayan an tashi wasan, sai Melaye ya kinkimo wani bidiyo ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce magoya bayan su na huce haushinsu a kan ‘yan wasansu.
“Magoya-bayan Kamaru suna jibgar ‘yan kwallonsu saboda sun sha kashi a hannun kasar Masar. Abin takaici.” - Dino Melaye.
Bidiyon ya yi kasuwa
Rahoton ya ce a dalilin Sanatan, bidiyo ya ratsa kafafen zamani. A shafinsa kurum, mutane kusan 500 sun maida martani, mutane 350 sun yi ta yayata sakon.
A dandalin Twitter, mutanen da suka nuna wannan bidiyon ya ba su sha’awa sun haura 1, 000.
Sama da mutane miliyan 2.8 suke bibiyar tsohon Sanatan a shafinsa na Twitter. Wannan ya sa ya yi tasiri wajen yada bidiyon yayin da ake buga gasar kofin AFCON.
Tsohon ‘dan majalisar ya kuma daura bidiyon a Instagram inda ya samu karbuwa bayan an kalle shi kusan sau 400, 000, an kuma bar masa martani sama da 2, 700.
Yayin da yake da mabiya miliyan 2.2 a Instagram, mutane fiye da miliyan 1.5 suke bibiyar Melaye a Facebook inda a nan ma dubban mutane sun ga bidiyon da ya sa.
Gaskiyar lamarin
Da The Cable ta bibiyi bidiyon, ta gano ba a wasan hakan ta faru ba. Wanda ya dauki wasan ya ce ba ayi rigima bayan an tashi kwallo tsakanin Masar da Kamaru ba.
Bayan an tashi wasan, magoya-bayan Kamaru sun fita daga filin kwallon Olembe salin-alin ba tare da sun tada tarzoma ba, akasin abin da Dino Melaye ya rubuta.
Bincike ya nuna cewa magoya-baya sun kutso cikin fili ne bayan wasan Aljeriya da Ivory Coast a filin kwallo kafa na Japoma da ke Douala domin nuna farin cikinsu.
Source: Legit.ng
================
Daga Jaridar isyaku.com
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakulabari
Facebook Facebook.com/isyakulabari
Rubuta ra ayin ka