Gwamnatin tarayya ta bakin hukumar lura man feturin saman kasa NMDPR ta tabbatar da cewa an samu matsala wajen sarrafa man feturin da aka sayarwa gidajen mai.
Hukumar NMDPR ta bayyana hakan ranar Talata inda tace adadi sinadarin 'Methanol' dake cikin feturin ya yi yawa.
A jawabin da ta saki, ta bayyana cewa an gano dan kasuwan man da yake raba wannan mai kuma za'a hukuntasa yadda ya kamata.
Hukumar tace:
"An gano man feturin mai sinadarin Methanol fiye da yadda ya kamata a gidajen mai a Najeriya."
"Methanol wani sinadari ne da ake karawa fetur don daidaita shi."
"Domin tabbatar da lafiyar motoci, an kwashe wannan gurbataccen man daga cikin jama'a, ciki har da tankunan man dake hanya yanzu haka."
Legit
================
Daga Jaridar isyaku.com
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakulabari
Facebook Facebook.com/isyakulabari