Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta samu izinin fara amfani da sabbin jiragen 'Super Tucano' wajen ragargazan yan bindiga masu garkuwa da mutane a fadin tarayya.
A shekarar 2021, Gwamnatin tarayya ta sayi sabbin jirage daga kasar Amurka.
Antoni Janar kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami SAN, ya bayyana hakan a shirin Good Morning Nigeria na tashar NTA ranar Talata, 4 ga Junairu, 2022.
Yace Gwamnatin tarayya ta samu izini daga wajen Amurka kuma ta yi alkawarin amfani da jiragen yadda ya kamata.
Yace yanzu haka ana kokarin katabta jiragen cikin kundin dokokin Najeriya.
A cewarsa:
"Muna fuskantar matsalar yan bindiga a Arewa maso yamma kuma shi yasa muka sayi makamai wajen yaki da su."
"Mun samu izinin amfani da Super Tucano. Yanzu muna shirin katabtashi cikin doka."
Source: Legit.ng
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
Rubuta ra ayin ka