An kashe Hausawa biyu aka banka wa gawarsu wuta a Akwa-ibom, duba dalili


Wata rigama ta barke a Afaha Oku da ke garin Ikpa a karkashin karamar hukumar Uyo cikin jihar wanda ya yi sanadin mutuwar wasu ‘yan jari bola guda biyu, The Punch ta ruwaito 

An tattaro bayanai akan yadda jama’a su ka taru wurin yi musu kisan ature saboda zarginsu da zama sanadiyyar mutuwar wani dan jihar, Anietie. 

Wani mazaunin yankin, wanda ya bukaci The Punch ta sakaya sunansa ya ce lamarin ya auku ne a ranar 2 ga watan Janairun 2022 da misalin karfe 9 na safe. 

Tushen lamarin 

A cewarsa: “Farkon abinda ya faru shi ne matasan kauyen ne su ka banka wa wasu Hausawa biyu ‘yan jari bola wuta bayan kama su da laifin halaka wani dan asalin kauyen Afaha Oku, Anietie bayan wani rikici ya hada su. 

“Anietie ya je amsar kayansa ne daga shagon wanki da safiyar Lahadi, sai dai yana hanyarsa ta komawa gida ya hadu da wasu Hausawa ‘yan jari bola dauke da wasu karafa da suka sace daga gidansu. 

An sanar da ni yadda ya tsayar dasu ya na tambayarsu abinda su ke yi a harabar gidan. Cikin fushi Hausawan su ka fara dukansa har sai da ya rasa inda kansa yake. Bayan dan’uwan Anietie ya hango yadda lamarin ya auku ne ya fara neman taimako.” 

A cewarsa mutane sun yi saurin isa wurin inda su ka yi ram da hausawan. Daga baya aka samu labarin mutuwar Anietie bayan wucewa da shi asibiti. Cikin fushi jama’a su ka hankada Hausawan cikin kwata tare da banka musu wuta inda su ka kone kurmus har lahira. 

Jami’in hulda da jama’an rundunar ‘yan sandan jihar, Odika MacDon ya tabbatar da aukuwar lamarin inda yace kwamishinan ‘yan sandan jihar, Andrew Amiengheme ya bayar da umarnin yin bincike akan lamarin. 

Sai dai kakakin ‘yan sandan ya nuna rashin jin dadinsa akan kisan inda yace dama matasan sun kai ‘yan jari bolan gaban hukuma ba tare da daukar mataki da hannayensu ba. 

MacDon ya bayyana yadda binciken da aka fara yi ya nuna cewa ‘yan jari bolan sun saci abubuwa a gidansu Anietie ne lokacin da mutane su ka wuce coci. 

Ya kara da cewa: 

“Kwamishinan ‘yan sanda ya bayar da umarnin yin bincike mai zurfi akan lamarin kuma ya hori jama’a da su guji daukar doka a hannunsu.” 

Source: Legit.ng 

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN