Yadda aka kwashe yara yan makaranta a cikin motar kwasar shara a Kano, duba mi ya faru


Yajin aiki da yan adaidaita sahu suke yi a jihar Kano na ci gaba da haifar da matsanancin kunci ga rayuwar al'umman jihar Kano musamman yara yan makaranta. Shafin isyaku.com ya samo.

Wasu hotuna sun nuna yadda yanzu yara yan makaranta ke neman a rage masu hanya har da amfani da motar kwasar shara.

Hotunan sun nuna yadda wasu yara yan makaranta a titin tsohuwar BUK kusa da kan Kwanar shiga Unguwar Dorayi suka hau wata motar kwasar shara domin a rage masu hanya bayan sun taso daga makaranta dik da rashin tsabtar motar kuma lamari da ke iya haifar da kamuwa da cuta ga yaran.

Tuni dai masana harkokin yau da kullum suka yi Allah wadai da rashin daidaito tsakanin Gwamnatin jihar Kano da yan adaidaita sahu, lamari da ya kai ga yajin aiki daga yan adaidaita sahu da kuma gazawar Gwamnati wajen samarwa jama'a mafita, sakamakon kunci da rashin adaidaita sahu ya jawo a bangaren sufuri ga talakawa a jihar.


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN