Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta damke wani Janar din Soja na karya kan zargin damfarar N270m (Milyan dari biyu da saba'in).
EFCC ta bayyana hakan ne a jawabin da ta saki tare da hotunan Sojan a shafinta na Tuwita.
Sojan Bogin mai suna Bolarinwa Oluwasegun ya yi ikirarin cewa Shugaba Buhari ya so ya zama Shugaban hafsan Sojin Najeriya.
EFCC ta ce
Jami'ar hukumar EFCC na shiyar Legas sun damke, Bolarinawa Oluwasegun, wani Janar din Sojan karya wanda yayi ikirarin Buhari ya zabeshi matsayin Shugaban hafsan Soji da zargin damfarar N270m."
Duk yunkurin da Legit Hausa tayi na samun karin bayani daga wajen hukumar EFCCC ya ci tura.
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari