Rikicin siyasar Kebbi: A baje koli na ayyuka tsakanin Adamu Aliero da Atiku Bagudu, talakawa su zama Alkalai, an zana ginshikai guda 5, duba ka gani



Bayan tabbatar tsagewar jam'iyar APC reshen jihar Kebbi zuwa bangaren Adamu Aliero da Atiku Bagudu, al'umman jihar Kebbi na ci gaba da hasashe tare da fadin albarkacin bakinsu dangane da yanayi da sabanin ra'ayin siyasa tsakanin Sanatocin guda biyu ya haifar a siyasar jam'iyar APC reshen jihar Kebbi. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Jama'a da dama na ganin samuwar rashin fahimta tsakanin yan siyarsa guda biyu alkhairi ne ga talaka, domin ko ba komai talaka ya san wanda ya fi kyautata wa rayuwarsa tsakanin mutanen guda biyu, kuma nan zai ja burki idan lokacin zabe ya zo.

Kazalika wasu masana harkar siyasar jhar Kebbi sun yi nuni da cewa hanya daya da za ta kawo karshen jayayyar karfin siyasa tsakanin Sanatotin guda biyu shi ne dukkansu su fito fili su baje kolin ayyukan da suka yi wa talakawan jihar Kebbi a zamanin mulkinsu a matsayin Gwamna.

Masanan sun ce talakawan jihar Kebbi ne da kansu za su zama Alkalai idan har aka yi wannan baje kolin ayyukan da Adamu Aliero da Atiku Bagudu suka yi wa jama'ar jihar Kebbi

Daga cikin ababen da masana suka bukata a saka a zaman manyan ginshikin maki a baje kolin ayyukan, sun hada da:

1. Yawan manyan ayyuka da Adamu Aliero ko Atiku Bagudu suka yi wa al'ummar jihar Kebbi, kuma alumma ke amfana da su, ko da nan da shekara 50 gaba.

2. Karko da ingancin ayyukan.

3. Wane mulki ne ya gina talakawa da suka zama wasu ababe a rayuwa kuma wane mulki ne ya talauta talakawan jihar Kebbi.

4. Wane mulki ne yan kasuwa da ma'aikatan Gwamnati suka fi samun walwala na tattalin arziki da rufin asiri na rayuwa.

5. Wane mulki ne talakawan jihar Kebbi suka fi samun tsaro.

Wadannan su ne kadan daga cikin ababen da masana harkar siyasar jihar Kebbi suka bukata daga manyan yan siyasar kuma kasancewa zance da ake gulma a kai a cikin al'umman jihar Kebbi a halin yanzu.

Ku biyo mu domin ci gaban wannan labari.....

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN