Labarin da aka yada ya nuna cewa mutumin ya kama matarsa tana sheke ayarta da wani kato kwanaki kadan bayan aurensu.
A cewar labarin da @chuddyOzil ya wallafa a shafinsa na Twitter, mutumin da matarsa sun yi aure ne a ranar 27 ga watan Disamba, 2021. Sai dai rikicin ya soma ne lokacin da mutumin ya kama matarsa da wani mutum a wurin da suke shakatawa.
Labarin ya ce ana daukar matakan kawo karshen auren nan kusa:
A cewar rubutun na Twitter:
"An yi aure (gargajiya da coci) a ranar 27 ga Disamba, 2022, an kama ta tare da daya daga cikin samarinta a ranar 5 ga Janairu 2021, suna luguden lebe a kwalbar giya a cikin wani yanayi na dadi. Mijin da umunna sun riga sun shirya bin hanyar al'ada. Aure ya kare!"
Legit
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
Rubuta ra ayin ka