Kungiyar masu tuka a daidaita sahu ta jihar Kano ta bayyana kudurinta na fadawa yajin aiki daga yau Litinin 10 ga watan Janairu. Wannan na zuwa ne bayan da kungiyar ta bayyana rashin jin dadinta ga yadda ake tafiyar da sana'ar a daidaita sahu a jihar.
Hakazalika, kungiyar ta koka kan yadda ake cin mutuncin masu sana'ar a jihar, inda kuma ta koka kan yadda mambobinta ke biyan haraji ba kan gado.
A cikin sanarwar da hukumar ta fitar wacce wakilinmu a Legit.ng Hausa, kungiyar ta bayyana wani gargadi ga mambobinta, inda tace:
"Gargadi ga duk wani dan a daidaita sahu matukin a daidaita sahu na jahar Kano, idan ka sake ka fito aiki ranar, to duk abin da ya faru da mashin dinka kai ka jawowa kanka. Saboda haka don Allah a bamu hadin kai."
Karin bayani na nan tafe...
Source: Legit.ng
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
Rubuta ra ayin ka