Jerin gwano da dandazon jama'ar Adamu Alito a garin Birnin kebbi |
Tsagin tsohon Gwamna kuma Sanata mai wakiltar Kebbi ta tsakiya a Majalisar Dattawa Sanata Adamu Aliero sun gudanar da taron buda ofishin jam'iyar APC a garin Birnin kebbi ranar Lahadi 9 ga watan Janairu 2022.
Wannan yana zuwa ne a daidai ranar da jam'iyar APC reshen jihar Kebbi karkashin jagorancin Abubakar Kana da shugaban jam'iyar na jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu ke tantance yan takara a Sakatariyar jam'iyar da ke kan hanyar Rima kusa da tsohuwar ofishin NITEL a Unguwar GRA, Birnin kebbi.
A daya bangaren kuma kimanin mita 400 daga Sakatariyar, tsagin Adamu Aliero suka buda wata Sakatariyar na APC a Bagudu House wanda basa nesa da juna kuma a kan titi daya.
An dauki tsatsaurar matakan tsaro yayin da jami'an tsaro suka datse hanyar da ke bi ta Sakatariyar jam'iyar APC reshen jihar Kebbi har da hanyoyin lunguna da ke iya bullewa zuwa Sakatariyar an datsesu.
Sabon ofishin APC tsagin Adamu Aliero a Bagudu House |
Kazalika an gan gungun jami'an tsaro jibge a kofar shiga Sabuwar Sakatariyar APC tsagin Adamu Aliero da ke Bagudu House.
Tsagin Adamu Alito sun gudanar da kasaitaccen taron buda Sakatariyar a filin Sukuwa da ke Unguwar Bayan Kara a garin Birnin kebbi. Lamari da ya haifar da yan kallo a garin Birnin kebbi da masana suka alakanta dandazon jama'a da lokacin zuwan shugaba Muhammadu Buhari yakin neman zabe na 2019 a garin Birnin kebbi.
Wani jigo kuma mai ruwa da tsaki a harkar siyasar jam'iyar APC reshen jihar Kebbi wanda a yanzu yake tsagin Adamu Aliero, ya ce :
" Taro da muka yi mun tabbatar da buda ofis na jam'iyar APC na asali. Mun tabbatar da cewa mu yan APC ne kuma muna tare da shugabancin Adamu Aliero. Mun tabbatar cewa za mu yi tafiya tare da jagorancin jam'iyar APC na kasa bisa ga biyayya. Mun kira magoya bayanmu su zauna lafiya kada su yarda su yi tashin hankali domin mai nassara baya fada".
Taron yan jam'iyar APC tsagin Adamu Aliero a filin Sukuwa |
Lamari da ya gudana a filin Sukuwa a garin Birnin kebbi ranar Lahadi 9 ga watan Janairu 2022, ya tabbatar da samun tsagi a jam'iyar APC reshen jihar Kebbi, kuma lamari ne da ya fallasa tabbacin rashin daidaito da mabanbantan ra'ayoyi da akidar jiga-jigan jam'iyar APC reshen jihar Kebbi kuma tabbacin bayyanar tsagin Aleiro da jama'a ke wa lakabi da tsagin "A" da na Bagudu da jama'a ke wa lakabi da tsagin "B" .
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari