Yanzu yanzu: Mahukunta sun rushe gidajen bayin Allah a Unguwar Kawara a garin Birnin kebbi, duba ka gani (Hotuna)Mahukunta a jihar Kebbi sun rusa gidajen bayin Allah a Unguwar Kawara da ke gabacin garin Birnin kebbi. Shafin Isyaku.com ya samo.

Lamarin ya shafi talakawa ciki har da gidan wasu marayu da mahaifiyarsa ta yi iya kokarinta na samar masu muhalli bayan rasuwar mahaifinsu.

Kazalika mun samo cewa wani da aka rusa gidansa mai suna Malam Yakubu, ya karbi bashin N1m a Banki wata biyu da suka gabata kuma ya rufe gidansa mako daya da ta gabata amma aka rushe gidan ranar Lahadi 15 ga watan Janairu 2022.

Malam Yakubu ya ce "Na shafe shekara 10 in tattalin kammala gina wannan gida a matsayina na talaka, amma an rushe mani gida, wannan ya yi kama ta mutuwa".

Sai dai shafin isyaku.com ya samo cewa mahukunta na zargin cewa mutane sun gina gidajen ne ba bisa ka'ida ba kuma a hanyar mota da ake shirin yi da zai fita zuwa filin sauka da tashin jiragen sama.

Kokarin mu na jin ta bakin wasu manyan jami'an Gwamnati da ke da alhakin bayani kan lamarin ya ci tura a halin yanzu. Domin dai basu amsa kiraye- kirayen wayar salula da muka yi masu ba.

Ku biyo mu domin jin cikakken rahotu kan lamarin daga bangarori da lamarin ya shafa da kuma bayanin mahukunta kan lamarin.


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakulabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN