Wani dan bindiga da ya yi kaurin suna a yankin Birnin Magaji da ke jihar Zamfara, Alhaji Auta, ya halaka a wani harin da sojojin saman Najeriya suka kai ta sama.
An kuma hallaka da dama daga cikin ’yan tawagarsa a yayin farmakin da suka kai wa sansaninsa da ke Jama’are Bayan Dutchi, a gundumar Nasarawa Mailayi a Jihar Zamfara, a ranar Asabar.
Majiyoyi da dama sun tabbatar wa jaridar Daily Trust rasuwar Auta amma sun ce ba a san adadin wadanda suka mutu a harin ba.
Auta na cikin kasurgumai hudu na ‘yan bindigar da ke ta’addanci a yankin.
Karin bayani na nan tafe...
Legit
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari