Hazikan matasa ma'abuta amfani da soshiyal midiya kan tafka wasu kurakurai da masana ke hasashen cewa za su iya zama lalura ga rayuwarsu ba tare da sanin dalili ko musabbabin faruwar lalurar ba.
Mafi yawan yan soshiyal midiya kan tallata yan takara na jam'iyun siyasa ba tare da sun yi amfani da kafar domin amfanin kansu ko na iyayensu ba.
Wasu daga cikin irin wadannan kura-kurai sun hada da:
1. Yi wa dan siyasa ko mai arziki addu'a kowane Juma'a ba tare da sun yi wa iyayensu addu'ar Juma'a ba.
2. Tallata makaryatan yan siyasa, da dora su kan karagar mulki ke zama bala'i ga rayuwar talaka sakamakon ayyukan yan soshiyal midiya wajen tallan irin wadannan mutane.
3. Wasu yan siyasa na amfani da yan soshiyal midiya domin cin zarafin mutanen kirki, bata wa abokan takara suna, kage, sharri da ababen da ke da alaka da haka da sunan siyasa.
4. Nuna isa, kasaita da rashin neman ilimin zamani wajen tafiyar da harkar tsarin soshiyal midiya kan zama sanadin rike dan soshiyal midiya a waje daya.
Wadannan kadan ne daga cikin ire-iren matsalolin da matasa da samari ke iya fuskantar a wajen tafiyar da harkar soshiyal mediya.
Domin samun ilimin yadda za ka yi nassara a rayuwarka na soshiyal midiya Latsa Nan ka tuntube mu Latsa Nan ka tuntube mu
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
Rubuta ra ayin ka