Yan daban siyasa sun lakada wa mai sukar Matawalle duka, sun farfashe motarsa


Makonni biyu bayan kai farmaki ofishin wata jaridar yanar gizo da gidan talabijin, wasu da ake zargin 'yan daban siyasa ne a ranar Juma'a sun kai mummunan farmaki kan mai sukar Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara inda suka ragargaza motarsa a Gusau.

An lakada wa Shamsu Kasida mugun duka kuma an farfasa motarsa yayin da ya tsaya a wani wurin cin abinci da ke kusa da gidan gwamnatin jihar a Gusau, Premium Times ta ruwaito.

Manajan daraktan gidan talabijin na Thunder Blowers, Anas Anka, ya zargi gwamnan jihar da daukar nauyin farmakin farko. Ya ce a tuhumi gwamnan a duk lokacin da mummunan lamari ya faru da shi ko ma'aikacinsa.

Wanda aka kai wa farmakin mai suna Shamsu Kasida, gagarumin mai sukar gwamnan ne a kafafen sada zumunta. Ya na goyon bayan Sanata Kabir Marafa, daya daga cikin abokan adawar Matawalle.

Daga Marafa har Matawalle 'yan jam'iyyar All Progressives Congress (APC), amma Marafa ya na sukar yadda aka mayar da shi da Abdulaziz Yari gefe a hedkwatar jam'iyyar mai mulki.

Wani abokin Kasida, wanda ya zanta da Premium Times a waya, Ismaila Salmanu, ya zargi cewa 'yan siyasa ne suka dauka nauyin harin.

"Kasida ya na tsaye a wani gidan cin abinci mai suna Yandoto yayin da 'yan daba suka fara dukansa. Suna dauke da miyagun makamai. Yayin da suke dukansa, daya daga cikinsu ya yi amfani da adda," yace.

Gidan cin abinci na Yandoto fitacce wuri ne a Gusau kuma mallakin Marafa ne sannan ya na titi daya da gidan gwamnatin jihar. Gidan cin abincin kai tsaye ya ka kallon gidan gwamnatin.

Salmanu ya ce 'yan daban sun tsaya da dukan Kasida ne bayan wasu mutane da ke wurin sun shiga. Amma kuma, 'yan daban sun farfashe gilasan motarsa kirar Honda Accord.

"Wasu daga cikin abokanmu da ke tare da Kasida yayin farmakin sun ce 'yan daban sun tsere zuwa cikin gidan gwamnatin bayan farmakin. Mun kai shi wani asibiti mai zaman kansa inda aka bashi gado. Ya samu miyagun raunika amma ba zan iya aiko da hotunansa yanzu ba," Salmanu yace.

Wata majiya wacce ta bukaci a boye sunan ta, ta ce 'yan ta'addan sun samu jagorancin gagarumin shugaban 'yan daban Gusau, Danda Jan Wuya.

Mai magana da yawun Matawalle, Zailani Bappa, ya ki amsa kiran da aka yi masa kan lamarin amma ya ce gwamnatin jihar ba za ta martani kan zargin mutanen da ke neman suna ba.

Legit Hausa

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN