2023: Rikicin APC na cigaba da jagwalewa, ta kacame tsakanin Bagudu da Aliero


Rikici ya na ci gaba da kamari tsakanin gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu da Sanata Adamu Aliero wanda hakan zai janyo rabuwar kawuna a jam’iyyar APC a jihar, Daily Trust ta ruwaito a ranar Lahadi.

Shugabannin jam’iyyar na kasa da jihar sun bayyana wa manema labarai cewa, daga Bagudu har Alieru su na da wanda suke son a tsayar takarar gwamna a jam’iyyar APC.

Rahotanni sun nuna yadda Bagudu wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin arewa ya ke so a daura antoni janar, Abubakar Malami a matsayin dan takara, yayin da Alieru wanda ya yi gwamna har sau biyu a jihar, yake son a tsayar da Yahaya Abdullahi, wanda shugaba ne na majalisar dattawa a dan takarar gwamnan jihar.

Daga Malami har Abdullahi ba su bayyana ra’ayinsu na tsayawa takarar gwamnan ba amma na kusa da su sun bayyana cewa lokacin da ya dace kawai suke jira.

Kudirin Aliero kamar yadda Daily Trust ta ruwaito a ranar Lahadi, ya janyo rabuwar kawuna a jam’iyyar APC reshen jihar Kebbi.

Yayin da gwamna Bagudu, Malami da mabiyansu suka rabe bangare, Sanata Alieru, shugaban majalisa da mabiyansa sun koma gefe guda.

A bangaren Alieru, akwai Bala Sani Kangiwa wanda aka tube a taron jam’iyyar daga shugaba, yayin da gwamnan ya ke da Abubakar Kana Zuru a matsayin shugaba na jam’iyyar. Yanzu haka akwai ofisoshin jam’iyyar na jihar guda biyu a Birnin Kebbi, babban birnin jihar.

Wani dan majalisa ya sanar da manema labarai cewa, Bagudu da Alieru sun janyo rabuwar kawuna a jam’iyyar duk da Alieru ya taka babbar rawa wurin tsayar da Bagudu a takarar gwamnan shekarar 2015, amma tun bayan nan suka bata.

“Ya kamata Aliero ya tsaya haka. Ya na so ya tsayar da shugaban majalisar jihar amma dan takarar gwamnan Malami ne. Hakan ya janyo rabuwar kawuna a jihar Kebbi,” a cewar majiyar wacce ta bukaci a sakaya sunan ta.

Ya kara da cewa, “akwai matsalolin da ka iya barkewa idan har APC a jihar Kebbi ta ki yin adalci. A wancan taron saboda son zuciya aka tube shugaban jam’iyyar sannan aka daura wani. Ba za mu bari hakan ya ci gaba ba."

Ba a samu damar tattaunawa da Bagudu ba, amma shugaban jam’iyyar na bangaren su ya ce ba ya da masaniya a kan dayan bangaren jam’iyyar APC a jihar Kebbi.

Legit Hausa

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN