Yadda rahotun sirri da ke nuna yiwuwar barkewar wani yanayi da ba a taba ganin irinsa ba ya sa aka dakatar da shirin janye tallafin man fetur


Bayanai su na zuwa a game da yadda shawarwarin tsaro suka tursasa gwamnatin Muhammadu Buhari ta lashe aman da tayi a kan tallafin fetur.

Jaridar Punch ta ce shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya hakura da maganar janye tallafin man fetur bayan ya yi la’akari da wasu shawarwari da ya samu.

Bayanan da jami’an tsaro suka ba Mai girma shugaban kasa shi ne za a barke da zanga-zangan da ya fi na EndSARS kamari idan har farashin man fetur ya tashi.

Wani jami’i da ya zanta da Punch ya ce da farko Muhammadu Buhari ya yi niyyar dabbaka sabuwar dokar IPA wanda zai jawo litar man fetur ya kara tsada.

Jami’in da bai bari a kama sunansa ba ya ce gwamnatin tarayya ta ji tsoron ‘yan adawa su yi amfani da wannan zanga-zanga, su kawowa APC matsala a 2023.

Rahoton da aka kai wa shugaban kasa

“’Yan sanda, DSS, NIA da ofishin NSA su kan aika rahoton tsaro ga shugaban kasa a game da abubuwa irinsu tallafin man fetur.”

“Rahoton da aka aikawa shugaban kasa ya nuna kungiyoyi su na shirin yin zanga-zangar da ya nunka na EndSARS kusan sau goma.”

“Ana hasashen litar man fetur zai tashi zuwa N350 idan farashi ya cigaba da tashi a kasuwar Duniya. Hakan zai jawo zanga-zanga.”

“Sun kuma jawo hankalin shugaban kasa a kan juyin-mulkin da ake ta yi a kasashen Afrika da yadda ‘yan adawa ke amfani da damar.”

“Wannan ya sa shugaban Najeriya ya dakatar da cire tallafin, ya bar wa duk gwamnatin da za ta zo wannan nauyi.” - inji majiyar.

Zanga-zangar #EndSARS

A shekarar 2020 an yi fama da zanga-zanga da bore a wasu yankunan Najeriya domin nuna rashin jin dadin yadda dakarun SARS suke cin zarafin mutanen kasar nan.

A wancan lokaci, kungiyar MURIC mai wayar da kan jama’a game da hakkokin musulmai, ta gargadi masu shiga zanga-zangar da su yi hattara da mugun nufin wasu.

Source: Legit.ng

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakulabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN