Abun mamaki: Kotu ta raba auren Rashidat bayan mijinta ya fada soyayya da kare, duba yadda ta faru


Wata yar kasuwa, Rashidat Ogunniyi, wacce ke tuhumar mijinta da nuna soyayya da kula ga karensa fiye da ita, ta samu abin da take nema a kotu.

Premium Times ta ruwaito cewa wata kotun Kwastumare dake zamanta a jihar Legas, ta datse igiyoyin auren mutanen biyu.

Akalin kotun, mai shari'a Adeniyi Koledoye, ya bayyana cewa rashin halartar wanda ake zargi zuwa kotun ba zai hana cigaba da sauraron Shari'ar ba.

Alkalin ya ce:

Tun da aka fara sauraron wannan ƙarar, wanda ake zargi bai girmama zaman kotu ba, saboda haka kotu ba ta da wani zaɓi da wuce ta datse auren baki ɗaya."

"Bisa haka kotu ta na mai sanar da cewa ta raba auren dake tsakanin Mista Kazeem Ogunniyi da mai É—akinsa Rashidat Ogunniyi, yau. Daga yanzun babu auren miji da mata tsakanin su."

"Kowa ne É—ayan su zai tafiiyar da harkokinsa daban, Kotu na muku fatan Alkairi a harkokin da kuka sanya a gaba."

Shin ma'auratan ba su da 'ya'ya ne?

Game da É—a guda É—aya da Allah ya albarkaci ma'auratan da shi, Kotun ta yanke hukuncin barin yaron a hannun matar, kuma ta umarci tsohon mijin ya rinka biyanta N10,000 na ciyarwa duk wata.

Kazalika, Alkalin kotun ya É—ora É—awainiyar karatun yaro a wuyan Mista Ogunniyi, da sauran harkokin jin daÉ—i na yaron.

Mijina ya fi kulawa da karensa

Tun da farko Rashidat ta nemi kotu ta raba auren wanda ya shafe shekara 12, inda ta yi ikirarin cewa mijinta ya fi kula da jin daÉ—in karensa fiye da iyalansa.

Matar tace:

"Kazeem ba shi da kulawa a matsayin miji da kuma uba, baya nuna soyayya gare ni da kuma É—an da muka haifa. Ya fi kula da lafiya, farin ciki da kuma rayuwar karensa."

Jami'an hukumar Kwastam dake aiki a Seme da Badagry sun cafke wata motar É—auko litattafan addini ta É—auko Hodar Iblis.

Kakakin kwastam, Hussaini Abdullahi, yace jami'an sun gano cewa Hodar ta kai darajar Naira Biliyan N3.9bm.

Source: Legit.ng

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakulabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN