Yadda jam'iyyar APC ta kama hanyar...


Wani binciken jaridar Punch ya ce kokarin da kwamitin sulhu na jam’iyyar APC ke yi na sasanta rikicin cikin gida a wasu jahohin jam’iyyar na fuskantar koma baya a wasu jihohi.

Tun a watan Yunin 2020 da aka kaddamar da kwamitin karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe, an ɗage taron sau da dama.

Rikicin ana ganin ya fi kamari a wasu jihohi kamar Osun, tsakanin gwamna Oyetola da ministan harkokin cikin gida na Najeriya Rauf Aregbesola, wanda ya kai ga ɗage zaɓen shugabannin jam'iyyar na jihar.

A Kwara kuwa har yanzu an gaza shawo kan gwamnan jihar AbdulRahman AbdulRazaq da kuma ɓangaren ministan watsa labaai na Najeiya Lai Muhammad.

A jihar Kano ma ana ci gaba da takaddama tsakanin tsagin gwamna Abdullahi Umar Ganduje da kuma na tsohon gwamna Malam Ibrahim Shekarau, inda ko wanne ɓangare ke cewa shugabancinsa ne sahihi.

Haka abun yake a Zamfara ma, inda ɓangaren tsohon gwamnan jihar Abdulazizu Yari ya bare da na Kabiru Marafa, sun kuma ƙalubalantar jagorancin gwamna Matawalle wanda ya koma jam’iyyar a baya bayan nan.

A makwabciyarta ma jihar Kebbi ana ci gaba da taƙaddama tsakanin ɓangaren gwamnan jihar Abubakar Atiku Bagudu da kuma na tsoon gwamna Adamu Aliero, wanda suka bude sabon ofishin jam'iyyar kwanan nan.

Alamu dai na nuni da cewa za a yi babban taron jam’iyyar ba tare da an sasanta wadannan bangarori ba, yayin da shi kansa kwamitin sulhun ke kokarin kammala aikinsa kwanan nan.

BBC

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN