IBB: Tun lokacin yakin basasa, har yanzu akwai karfe a kirji na


Tsohon shugaban kasan Najeriya na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida, ya bayyana cewa har yanzu ya na da ragowar karfe a cikin kirjinsa tun wanda ya shigesa a yakin basasa.

An yi yakin basasa tsakanin shekarar 1967 zuwa 1970 a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

A yayin tattaunawa da Trust TV, tsohon dan siyasan mai shekaru tamanin a duniya ya tuna illolin da yakin basasa ya yi ga lafiyarsa.

"Ya faru a shekarar 1969. Muna kan hanyar mu ta zuwa Umuahia yayin da aka bude mana wuta awani wuri da ake kira Uzokoli. A hakan ne karfen ya shiga kirji na a bangaren dama, ya kusa taba min huhu ko kuma in ce ya taba, a haka ne na fara fama da ciwon," yace.

Tsohon shugaban kasar ya ce a yayin da ya je asibiti, likitoci sun shawarce sa kan cewa ya na da zabi a cire karfen ko kuma a bar shi, amma zai iya damun shi a gaba. Sai dai ya yanke shawarar a bar karfen a jikinsa.

"A wannan lokacin, na yanke shawara. Likitocin sun ce za su iya cire shi amma zan iya barin shi. Sai dai idan na tsufa, zan iya samun matsala kuma na yanke hukuncin in bar shi a hunhu na har in tsufa," yace.

IBB ya kara da cewa, duk da karfen ba wani damun shi ya ke ba da ya cika shekaru tamanin, ya na jin cewa akwai abu a cikin jikinsa, kuma hakan kadai ya na da firgitarwa.

Ya ce, "A gaskiya ba wata matsala bace gare ni yayin da na ke cika shekaru tamanin amma kuma ina jin shi. Sanin cewa akwai abu a jikin ka akwai firgitarwa."

Legit Hausa

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN