Yadda Jami'an tsaro suka yi wa yan bindigan jihar Niger dagargazar Allah kara sun kwace dabbobi 500
Jami’an tsaro na Jihar Neja sun samu nasarar halaka ‘yan bindiga da dama da suka dade suna addabar wasu garuruwan da ke karkashin karamar hukumar Munya da Shiroro da ke jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Ayyukan jami’an tsaron sun janyo an samu nasarar kwace dabbobi 500 a garin Kuchi, Galadiman-Kogo, Allawa da garin Erena da ke karkashin karamar hukumar Munya da Shiroro.

An kwashe dabbobin sannan aka garzaya da su Minna, babban birnin jihar da taimakon mafarauta.

Shanu biyar sun mutu kafin a isa dasu Minna saboda matsewar abin hawan da aka zuba su ciki da kuma nisa.

An samu shanu 300 da tumaki fiye da 100

Kwamishinan harkokin kananan hukumomi da harkokin cikin gida na jihar, Emmanuel Umar ya shaida yadda aka samu nasarar kwaso dabbobin wadanda ciki akwai shanu 300 da tumaki fiye da 100.

A cewarsa za a ajiye dabbobin karkashin kulawar Ma’aikatar Dabbobi ta Jihar.

A cewarsa, yayin da aka halaka ‘yan bindiga da dama, wasu jami’an tsaro sun rasa rayukansu amma bai sanar da yawansu ba.

Ya ce yanzu haka ana ta kokarin ganin yadda za a tallafa wa iyalan jami’an tsaron da aka halaka.

Kwamishinan ya kula da yadda gwamnatin jihar ta gama shirya hanyoyin da zata gano asalin masu dabbobin don a basu ko kuma su shiga cikin dukiyar jihar.

An samar wa rundunar ‘yan sandan sabbin kayan yaki da motoci don su tallafa wurin yakar ta’addanci a jihar

Umar ya kula da yadda rashin tsaro a jihar zai gyaru matsawar aka kawo karshen ‘yan bindiga, masu satar dabbobi, masu garkuwa da mutane da sauransu.

Sai dai Daily Trust ta tattaro bayanai akan yadda rundunar ‘yan sandan Jihar Neja ta gama samun kayan yaki daga hedkwatar ‘yan sandan don kawo karshen ‘yan ta’addan.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun ya tabbatar da cewa an samar da kayan yaki har da ababen hawa biyar tare da motocin yani daga hedkwatar ‘yan sanda.

A cewarsa ana fatan sabbin kayan yakin za su taimaka wa rundunar wurin kawo karshen ta’addanci a jihar.

Source: Legit.ng

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakulabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN