Tonon asiri: Yadda aka kwace wa isyaku.com shaguna 3 aka kulla masa sharri sau 8, CID suka kama shi a Birnin kebbi, duba ka gani


Kadan daga cikin irin nau'in cin mutunci da Malam Isyaku Garba Mawalafin shafin labarai na isyaku.com ya fuskantar a hannun yan siyasar jihar Kebbi daga 2014 zuwa yau.

1. An kwace shugabancin kungiyar masu sayar da waya da gyaran wayar salula daga hannunsa duk da yake shi ya kirkiro ta ya rada mata suna kuma ya assasa ta. Ba laifin komai, ba takardar  zargin aikata laifi ko korafi. An ce kawai Malam Isyaku dan Zuru ne.

2. An kulla masa sharri kasancewa mai cire security na wayoyin sata da kuma kazafin ba wani yaro N500 domin ya saye kwaya don ya je ya kashe wani mai sayar da waya, lamari da bai ji kuma bai gani ba. Sakataren kungiyar da shugabanta da wani bakatsine ne kan gaba wajen kitsa wannan sharri tare da hadin baki da wasu jami'ai, Lauya da yan siyasa.


CID daga Shelkwatar yansandan jihar Kebbi bisa umarnin Kwamishinan yansanda na waccan lokaci sun kama Malam Isyaku bisa wannan zargi, sun yi bincike karkashin jagorancin Mataimakin Kwamishinan yansanda na sashen SCIID. Allah ya kiyaye ni daga sharrin da aka kulla.

3. Shugaba tare da yan kungiyar waya karkashin jagorancin wasu yan siyasa sun yi sanadin kwace shagunan Malam Isyaku guda uku daga Olumbo plaza a kan titin Ahmadu Bello bayan kitsa kazafi kala-kala, sharri, da makircin kin karbar kudin hayansa da gangan sai suka je Kotun haya (Rent Tribunal) suka ce bai biya kudin haya bane.

4. Bayan bullar Labarin matar da aka yi zargin ta tayar wa wani dan siyasa hankali a wayar salula daga Yauri kan hakkin fanshon mahifinta. An yi yunkurin amfani da yan daba domin su farmaki Malam Isyaku, a lokaci daya kuma an so a yi amfani da wasu jami'ai domin tursasa wa Malam Isyaku. (Dogaro da bayanan sirri)


5. Idan baku manta ba, bayan kin biyan kudin aiki da gangan daga wani dan siyasar Masarautar Zuru tsakaninsa da Malam Isyaku, lamari da ya jawo martanin kare kai, wannan dan siyasa, ta hannun PA da ke masa aiki, ya umarci Malam Isyaku ya kwashe kayansa ya bar jihar Kebbi kafin ya dawo daga Abuja.

6. Wani Dan siyasar kasar Zuru ya bukaci wata ma'aikata ta hana Malam Isyaku wallafa labarai kwata-kwata, amma Kwamishinan ma'aikatar ya yi amfani da hikima wajen sasanta lamarin.

7. Kazalika wani dan siyasa ya yi barazanar sa a kama Malam Isyaku idan yan kungiyar waya sun yi zanga zangar lumana kan zargin rashin adalci wajen rabon N40m da aka ba kungiyar rance.


8. Bayanan airri sun yi nuni da cewa yan siyasa sun hada kansu domin ganin Malam Isyaku bai amfani da wani lamari na alfarma ko bukata ba a tsarin wannan tafiya tasu a fadin jihar Kebbi, saboda labari da Jaridarsa ta fitar na matar Yauri da dan siyasa ya sa aka kama da kuma labarin dukan da aka yi wa Mawakan APC a jihar Kebbi

Malam Isyaku ya taimaka wa Gwamnatin jihar Kebbi, shugaba Buhari da jam'iyar APC wajen kaiwa ga nassara ta hanyar amfani da shafukansa na labarai. 

Wannan shi ne kadan daga cikin sakayyar da yan siyasa suka yi wa Malam Isyaku a jihar Kebbi.


Ingantattun bayanan sirri na nuni da cewa wadannan yan siyasa har yanzu sun dukufa wajen neman yadda za su cutar da Malam Isyaku saboda mumunar riko na al'adar mugunta tare da ganin cewa bai amfana da komi ba na alfarma ko hakki daga mulkinsu a jihar Kebbi.

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN