Tap di: Yadda Dattijo ya kirkiri risho mai aiki da ruwa marmakin kalanzir ko gas, duba ka gani


Yayin da ake tsananin bukatar mafita ga tsadar rayuwa a Najeriya, wani dattijo ya jima da samar da sauki a wani bangaren; ta hanyar samar da risho din girki mai amfani da ruwa.

Makwanni kadan da suka gabata ne kafafen sada zumunta suka cika da ta'ajibi ganin wani dattijo yana amfani da ruwa wajen samar da makamashi.

Wannan yasa, Legit.ng Hausa tayi tattaki zuwa inda wannan dattijo yake a jihar Gombe domin jin ta bakinsa da kuma tsare-tsaren da yake yi a nan gaba.

A tattaunawarsa da wakilinmu, Malam Muhammad Hadi Usman, ya shaida cewa, ya yi wannan aiki ne shekaru uku da suka gabata, don haka ya ma kirkiri abubuwa da dama bayan wannan risho.

Yayin da yake yiwa wakilinmu bayani kan yadda ya samar da wuta ta hanyar, Malam Hadi yace:

"Wutan lantarki kanta, idan aka yi dogon bincike ai daga ruwa take, domin kuwa an samu wutar lantarki ne daga walkiya da tsawa ta araduwa da bahaushe yake fada daga sama.

"Misali na farko da zaka fahimta yanzu, idan aka ce damuna ta wuce, amma ai akwai gajimare, to amma me yasa ba a yin walkiya ba a yin tsawa? Saboda ba ruwa a cikinsa."

Ya kara da cewa, duba da wadannan misalai, ya rage wa mutum ya yi amfani da iskar oxygen da ke yawa domin tara dabarun samar da wutar, kamar dai yadda ya yi.

Hakazalika, ya ce wannan ba sabon abu ne a wurinsa ba, domin bayan wannan ya yi abubuwa da dama, tun da a cewarsa, risho din ya fi shekara uku da kira.

Game da batun risho mai amfani da ruwa, Malam Hadi ya ce ya zauna sun yi shawari da lauyoyinsa da masu bashi shawari cewa, ba yanzu ne lokacin da ya dace ya sayar da fasahar ba.

Na fara kirkira tun 1971, na kirkiri jirgi mai saukar ungulu, inji Malam Hadi

Da aka tambaye ko yaushe ya fara irin wadannan kirkire, Malam Hadi ya ce, akalla ya shafe shekaru sama da 50 yana kan wannan aiki na kirkirar ababen ban mamaki, inda ya shaidawa Legit.ng Hausa cewa:

"Fara kirkirar abu na sa kasuwa, kuma mutane su gani su ce sun ji mamaki na fara tun karshen 1971. Domin a 1970 da 1971 ni makanikin besfa ne.

" Ta hanyar gyaran besfa, nayi tunanin nayi abin da wani bai taba yi ba a gyaran besfa da aikin besfa.

"A binciken da nayi na gano zan iya kirkirar jirgi helikofta da injin besfa. Na yi shi kuma ya tashi a karshen 1972."

Sai dai, a jawabansa ya ce bayan tashin jirgin an samu matsala jirgin ya fadi a gidan wani, lamarin da ya jawo masa tsaiko ya dakata da aikin bayan samun sabani da iyalansa.

Daga wannan lokacin, Malam Hadi ya jingine aikin gyaran besfa domin kama wata harkar daban, wacce ita mai cike da ban mamaki ce.

Malam Hadi ya ce ya yawata jihohi da kasashen ketare yana koya wa matasa da dukkan masu sha'awa wannan fasaha, kuma yana ci gaba da yi.

Babban abin da yake kara jan hankalin mutane a cewarsa, shi ne yadda bai taba shiga aji domin karatun ilimin zamani ba, amma ya iya turancin da zai iya bincikar littafan kimiyya da fasaha.

Legit Hausa

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN