Da duminsa: Yan bindiga sun sake kai hari Kaduna, sun tafka mugun aiki, duba ka gani


Wasu ‘yan bindiga a kan babura, kowannen su dauke da mutum2, sun kai hari a yankin Gbagyi Villa a daren ranar Litinin din da ta gabata. 

Yankin dai yana kan hanyar zuwa matatar mai ta Kaduna ne, inda suka kashe mutum daya tare da yin garkuwa da matarsa da wasu. 

Ya zuwa yanzu, 'yan jarida suna jiran martanin hukuma daga hukumomin tsaron kasar nan, kamar yadda Vanguard ta rahoto. 

A cewarsa: 

“Lokacin da suka shigo cikin jama’a, mutane suna gudu amma mutumin da ya yi kama da ‘yan banga ya tsaya yana kokarin yin waya da wani abu kamar wayar walkie talkie. ‘Yan bindigar sun harbe mutumin a ka. Ya fadi ya mutu,

” Ya yi zargin cewa baya ga matar marigayin da ‘yan bindigar suka sace, sun kuma yi garkuwa da wasu mazauna unguwar sama da 10 a wani samame da ya dauki sama da sa'a daya. 

Jaridar Punch ta rahoto cewa wasu yan bindiga sun yi garkuwa da Dorcas Vem, matar mataimakin shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin Filato, Silas Vem. 

Haka nan kuma, a wani harin na daban, yan bindiga sun sace Dakta Samuel Audu, daraktan ma'aikatar lafiya ta jihar Filato. 

Majiyoyi daga fadar gwamnatin jihar Filato dake Jos, da kuma hedkwatar ma'aikatar lafiya sun tabbatar da faruwar lamarin ranar Talata. 

Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN