Da duminsa: An cafke miyagu masu fasakwabrin muggan makamai daga kasar Nijar zuwa Najeriya, duba yadda ta faruJami'an tsaro sun samu nasarar kame wasu masu aikin shigo da muggan makamai cikin kasa Najeriya daga makociyarta Nijar.

Jami'an da suka yi wannan bajinta na aiki ne a yankin Dakwaro, a jihar Maraɗi, dake Jamhuriyar Nijar, kamar yadda Aminiya Hausa ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa jami'an sun damke mutanen ne dumu-dumu, yayin da suke yunkurin safarar wasu makamai zuwa Najeriya.

Gwamnatin Maradi ta yaba wa jami'an

Bayan samun labarin abin da ya faru, gwamnan jihar Maradi, Shu’aibu Abubakar, ya garzaya yankin Dakwaro, inda aka kame mutanen, kuma ya jinjina wa jami'an bisa wannan nasara.

Gwamnan ya nuna jin daɗinsa da kuma rokon jami'an tsaron su cigaba da kokarin dakile ayyukan irin waɗan nan mutanen.

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta daɗe da ɗaukar tsauraran matakan yaƙi da kuma kawo ƙarshen masu fasakwaurin makamai zuwa wasu ƙasashe, musamman waɗan da ke maƙwaftaka da Nijar.

Wane mataki gwamnatin Nijar ke ɗauka?

Legit.ng Hausa ta gano cewa a baya-bayan nan sai da gwamnatin Nijar ta tsare wasu ma'aikatan ta bisa zargin hannu a wannan aika-aika ta safarar makami ba bisa ƙa'ida ba da kuma haramtattun kwayoyi.

A ɗaya bangaren kuma, gwamnatin Najeriya na ta faɗi tashin magance shigo da makamai ba bisa ƙa'ida ba daga wasu ƙasashe dake maƙwaftaka.

A halin yanzun, Najeriya na fama ayyukan ta'addancin yan bindiga a wasu jihohin arewa maso yamma.

Source: Legit.ng

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN