Sojin Burkina faso sun kama shugaban kasar sun tsare shi, duba dalili da halin da ake ciki


Rahotanni na cewa sojojin da ke adawa da gwamnati a Burkina Faso sun tsare Shugaban Ƙasar Roch Kabore.


Wasu dakarun ƙasar ta Afirka ta Yamma sun nemi a kori wasu manyan jami'an soja da kuma samar da ƙarin kayan aiki don yaƙar masu iƙirarin jihadi.

An jiyo harbe-harbe a kusa da fadar shugaban ƙasa da kuma wasu barikin soja ranar Lahadi da dare a Ouagadougou babban birnin ƙasar.

Sai dai gwamnati ta musanta labarin yunƙurin juyin mulki ko kuma cewa an kama shugaban ƙasar .

Rahotanni na cewa ana tsare da Shugaba Kabore ne a wani sansanin soja.

Kazalika, sojoji sun kewaye gidan talabijin na gwamnatin ƙasar.

 ÆŠaruruwan mutane ne suka fito zanga-zangar nuna goyon baya ga sojojin duk da dokar hana fita da aka saka, sannan suka dinga Æ™ona ofisoshin jam'iyya mai mulki.

Bidiyon da aka rika yadawa a babban birnin kasar ya nuna wasu motoci masu sulke - wadanda rahotanni suka ce na fadar shugaban kasa ne - dauke da harbe-harben bindiga kuma an bar su a kan toituna.

Wakilin BBC Simon Gongo da ke Ouagadougou ya ce birnin ya yi tsit. Sai dai sojoji sun kewaye gidan talbijin na kasar.

An ga motocin da ake tunanin na fadar shugaban kasar ne dauke da harbin bindigogi

A ranar Lahadi Ministan Tsaro Janar Barthelemy Simpore ya musanta batun tsare shugaban ƙasar da kuma yadda hatsaniyar ke faruwa.

Gidan talabijin ɗin ƙasar kuma ya bayyana harbe-harben da aka ji da cewa wasu tsirarin sojoji ne maimakon babban rikici ko kuma juyin mulki.

Yayin da layukan intanet ba sa aiki yadda ya kamata, har zuwa safiyar Litinin ana zaune cikin ɗar-ɗar a babban birnin ƙasar, sakamakon babu wani bayani daga gwamnati ko kuma sojoji.

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye.

Rahotun BBC

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakulabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN