Da duminsa: An shiga firgici a Plateau yayin da yan bindiga suka farmaki jama'a, suka yi mugun barna


Mazauna kauyen Dung da ke karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato sun shiga jimami bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a wani wurin da ake hakar ma’adinai, inda suka kashe mutane hudu, Channels Tv ta ruwaito.

‘Yan bindigar sun kai farmaki wurin hakar ma’adinan ne a ranar Asabar din da ta gabata, inda suka harbe ma’aikatan har lahira, lamarin da ya tilastawa rundunar ‘yan sandan jihar ta tura karin jami’anta zuwa yankin.

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Gabriel Ubah ya fitar ranar Lahadi, ya ce an tura dakarun ne domin dakile tabarbarewar doka da oda.

Kakakin ‘yan sandan ya bayyana cewa rundunar ta fara gudanar da bincike da nufin kamo 'yan ta'addan.

Lokacin da aka tambayi jami'in ko hukumomin 'yan sanda na sane da harin, ya ce:

"Eh, rundunar tana sane da abin da ya faru a Dung.

“Nan take ‘yan sanda suka garzaya wurin da lamarin ya faru. Sai dai abin takaicin shi ne, wasu ‘yan bindiga da ba a san su ba sun kashe mutane hudu da suka je wurin hakar ma’adanai. An tsaurara matakan tsaro a yankin.

"A halin da ake ciki, ana ci gaba da gudanar da bincike don gano lamuran da suka shafi mutuwarsu da kuma kama wadanda suka aikata wannan mugun aikin."

A halin da ake ciki, dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Jos ta Kudu/Bassa a majalisar wakilai ta kasa, Dachung Musa Bagos, ya yi Allah wadai da lamarin.

Dan majalisar a wata sanarwa da kakakinsa Danja Dafwam Yaks ya fitar a ranar Lahadi, ya ce:

“Na fusata da kuma hasala da kashe-kashen da ake yi a mazaba ta da kewayenta. Ina so in bayyana cewa zan ci gaba da magana kan wadannan munanan dabi’u na mashahuran 'yan ta'adda a cikinmu har sai an kawar da su duka."

Haka kuma ya roki gwamnatin tarayya da na jihohi da su umarci jami’an tsaro da su tunkari matsalar rashin tsaro a fadin jihar da kasa baki daya.

Wani mazaunin yankin ya shaidawa jaridar Tribune cewa, harin na iya zama na daukar fansa daga Fulani, kasancewar an tsinci gawar wani yaro Bafulatani a yankin.

A wani labarin, rundunar OPSH yayin kokarin ganin ta samar da zaman lafiya a jihar, wasu yankunan Jihar Kaduna da Jihar Bauchi ta samu nasarar halaka wasu masu garkuwa da mutane 3 a Jihar Plateau inda ta kwace makamai a hannun su, The Guardian ta ruwaito.

Kakakin rundunar OPSH, Manjo Ishaku Takwa a wata takarda da ya saki jiya ya ce jami’an rundunar sun samu nasarar ragargazar wadanda ake zargin suna cikin ‘yan gidan yarin da suka tsero a ranar 28 ga watan Nuwamban 2021.

Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakulabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN